Sheikh Mujibur Rahman galibi ana taqaitawa da Sheikh Mujib ko Mujib, wanda kuma aka fi sani da Bangabandhu, shi ne ya kafa Bangladesh. Ya fara zama shugaban gwamnatin wucin gadi na Bangladesh tsakanin watan Afrilu a shekara ta 1971 zuwa watan Janairu, shekarar 1972.